Connect with us

Kiwon Lafiya

Kananan yara 5,000 ka iya rasa rayukansu saboda yunwa- Care International

Published

on

Jami’an ayyukan agaji a kasar Somalia, sun yi gargaɗin cewa ƙanana yara kusan dubu 5 ne ke cikin haɗarin yiwuwar rasa rayukan su saboda yunwa, a sakamakon rashin samun abinci mai gina jiki.

Cikin rahoton da ta fitar, ƙungiyar bayar da agaji ta Care International ta ce adadin yara ƙanana da suke fama da yunwa a Somalia ya ƙaru zuwa miliyan 1 da dubu 800, kamar yadda wani rahoton na daban da Majalisar Ɗinkin Duniya ta wallafa a ƙarshen watan Maris kan halin da ake ciki a ƙasar ta Somalia ya nuna.

A cewar rahoton na baya bayan nan, matsalar ƙarancin abinci na ƙaruwa cikin gaggawa fiye da hasashen da ƙwararru suka yi, saboda matsalolin Fari da kuma ambaliyar ruwan da suka raba kusan mutane miliyan guda da muhallansu.

Yazu haka ƙananan yara dubu dubu ɗari 479 ake fargabar za su fuskanci matsananciyar Yunwa da kuma haɗarin rasa rayukansu, idan har ba a kai musu agajin gaggawa ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!