Labarai
Kano: Ƴan bindiga sun yi garkuwa da ɗan uwan minista Nanono
Wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da ɗan uwan ministan noma Alhaji Sabo Nanono.
Ƴan bindigar sun shiga ƙauyen Tofai da ke garin Zugaci na ƙaramar hukumar Gabasawa da ke Kano ɗauke da bindigu da misalin ƙarfe 2 na daren Lahadi.
Sun kuma yi awon gaba da ɗan uwan ministan noma mai suna Malam Babawuro Tofai.
Wani makusancin Malam Tofai mai suna Ibrahim Da’u Joɗa ya shaida wa Freedom Radio cewa ƴan bindigar sun karya wani mutum guda ɗaya.
Mun tuntuɓi jami’in hulɗa da jama’a na ƴan sandan Kano DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa wanda ya ce suna bincike a kai.
You must be logged in to post a comment Login