Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Garkuwa da mutane: An sako matar dagacin da aka sace a Kano

Published

on

Ƴan bindiga sun sako matar dagacin garin Tsara na ƙaramar hukumar Rogo da ke Kano, bayan kwanaki 22 da sace ta.

Wani makusancin dagacin da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa Freedom Radio cewa, an sako matar bayan da aka biya kuɗi har miliyan biyu.

Ya ce “An tura wakilin dagaci da ɗan uwan matar domin su kai kuɗin zuwa dajin birnin gwari”.

Sai dai ƴan bindigar sun karɓe kuɗin tare da tsare mutanen.

A ranar Lahadi ne matar da wakilin dagacin suka samu kuɓuta.

Ya ce, har yanzu ɗan uwan matar yana hannun ƴan bindigar.

Shi kuma wakilin dagaci Malam Idi Liman yana asibitin garin Gwarzo sakamakon raunikan da suka yi masa.

Ita kuma matar dagacin Hajiya Asiya Shu’aibu, ana ci gaba sa bata kulawa a gida, kasancewar har kawo ranar Laraba ba ta dawo hayyacinta ba, a cewarsa.

Matar dagaci Hajiya Asiya Shu’aibu mai shekara 40.

A watan Janairun da ya gabata ma ƴan bindiga sun yi garkuwa da dagacin garin Karshi da ke ƙaramar hukumar ta Rogo.

Labarai masu alaka:

Masu garkuwa da mutane sun ɓulla a Kano

Wani matashi yayi garkuwa da wani yaro a Kano

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!