Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kano: Ɗaliban Sakandiren Dawakin Tofa sun tarwatse cikin dare

Published

on

Rahotanni daga garin Dawakin Tofa da ke nan Kano na cewa ɗaliban makarantar Sakandiren kimiyya ta garin sun tarwatse.

Lamarin ya faru ne a cikin daren Jumu’ar nan yayin da ɗaliban suka hango wasu Fulani ta bayan makarantar.

Hakan ne ya sanya ɗaliban suka fantsama cikin gari domin neman tsira.

Wani mazaunin garin ya shaida wa Freedom Radio cewa, sun ga ɗaliban na kutsowa cikin gari a guje inda suka basu masaukai a gidaje da kuma babbar makarantar firamare ta garin.

A cewar sa, tuni jami’an ƴan sanda suka yiwa makarantar ƙawanya sannan suka kewaye makarantar firamaren da aka killace ɗaliban.

Mun tuntuɓi Kwamishinan ilimi na jihar Kano Alhaji Sanusi Sa’idu Ƙiru amma bai ce komai ba a kai.

Sai dai wata majiya mai tushe a ma’aikatar ilimi ta Kanon ta shaida mana cewa, Fulani ne ke biki a wani ƙauye da ke gefen makarantar.

Kuma babu wutar lantarki a don haka suke haska fitilu suna yin maganganu, a daidai lokacin kuma ɗaliban sun tashi daga karatun dare, hakan ne kuma ya firgita ɗaliban.

Mun tuntuɓi mai magana da yawun ƴan sandan Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa amma bai ɗauki kiran wayar da muka yi masa ba har sau biyu.

Mun kuma aika masa da saƙon kar-ta-kwana amma har kawo lokacin da muke haɗa wannan rahoto babu amsa.

Wannan dai na zuwa ne, ƙasa da makonni biyu bayan da Gwamnatin Kano ta rufe wasu makarantun kwana da ke wajen birnin Kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!