Connect with us

Labarai

Kano: Ɗaurarru 52 sun fara rubuta jarabawar NECO da NABAIS

Published

on

Aƙalla ɗaurarru 52 sun fara rubuta jarabawar NECO da NABAIS a Kano

Aƙalla ɗaurarru 52 da ke gidajen ajiya da gyaran hali a Jihar Kano sun fara rubuta jarabawar kammala sakandare ta NECO da kuma ta Hukumar Kula da Ilimin Larabci da Addinin Musulunci (NABAIS) ta shekarar 2026.

Mai magana da yawun hukumar a jihar Kano, CSC Musbahu Lawan Kofar Nassarawa, ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa ta murya da ya aikewa manema labarai.

Ya ce daga cikin ɗaurarrun akwai maza 41 da mata 11, waɗanda aka zabo daga cibiyoyin ajiya da gyaran hali daban-daban na jihar domin rubuta jarabawar.

A cewarsa, wannan shiri na daga cikin ƙoƙarin Hukumar Gidan Gyaran Hali na amfani da ilimi wajen gyara halayen ɗaurarru tare da shirya su domin komawa cikin al’umma bayan kammala wa’adin hukuncinsu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!