Connect with us

Labarai

NBA ta zargi ƴan Sanda da tsare wani lauya ba bisa ƙa’ida ba

Published

on

Ƙungiyar Lauyoyi ta Najeriya NBA reshen jihar Kano, ta zargi Rundunar ƴan Sandan Jihar da tsare wani lauya Barista Mustapha Abubakar Adam ba bisa ƙa’ida ba.

NBA, ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar Barista Sani Ammani, ya fitar a yau Juma’a.

Sanarwar ta bayyana cewa an tsare lauyan ne a Sashen binciken manyan laifuka na rundunar ƴan sandan Kano a ranar 30 ga Yunin bana, bayan ya nuna rashin jin daɗinsa kan hana shi shiga domin kare wanda ya ke wakilta, yayin da ake barin wasu mutane suna shiga ba tare da tsaiko ba.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, daga bisani an sake shi da tsakar dare bayan shugabannin ƙungiyar sun shiga tsakani.

Haka kuma, sanarwar ta kuma ce shugabannin NBA na jihar Kano na NBA Ungogo sun gana da Kwamishinan ƴan Sanda da mataimakinsa mai kula da sashen binciken manyan laifuka domin sasanta lamarin.

Sannan ƙungiyar ta ce, ta samu umarnin kotu da ya hana sake kama lauyan, amma daga bisani an gayyace shi domin gurfana a gaban Kotun Majistare mai lamba 54 da ke Gyadi Gyadi

Kungiyar tayi kira ga mambobinta su halarci zaman kotun domin nuna goyon baya ga lauyan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!