Connect with us

Labarai

Gwamnan Kano ya bukaci EFCC da ICPC su sanya ido kan rabon takin noma a jihar

Published

on

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya umarci Hukumar Yaki da Masu Yi Wa Tattalin Arziki Zagon Kasa (EFCC) da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) su sanya ido kan rabon taki da za a raba domin tallafawa manoma don ganin an yi adalci.

 

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, an ce gwamnan ya ba da wannan umarni ne yayin kaddamar da rabon manyan motoci 150 na takin zamani ga manoma a kananan hukumomi 44 na jihar.

 

Gwamna Yusuf ya ce shigar da EFCC da ICPC cikin shirin zai taimaka wajen tabbatar da cewa takin ya isa ga manoman da suka cancanta tare da dakile karkatar da shi, boyewa ko sauran almundahana.

 

Ya kuma gargadi shugabannin kananan hukumomi da su gudanar da rabon cikin gaskiya da rikon amana, yana mai jaddada cewa duk wanda aka kama da karkatar da takin ko hana shirin nasara zai fuskanci hukunci bisa doka.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!