Labarai
Kano 9 Kids: Yara 113 aka sace daga Kano zuwa Kudu – Kwamitin bincike
Kwamatin bada shawarwari kan sace-sacen yara ‘yan asalin jihar Kano zuwa wasu daga cikin jihohin kudancin kasar nan ya ce zai fara daukan hanyoyi biyar cikin 46 da ya mikawa gwamnatin jihar a makon daya gabata da zai aiwatar da aikin magance matsalar satar yaran.
Shugaban kwamatin Justice Wada Umar Rano, ne ya bayyan hakan yau yayin da yake zantawa da manema labarai game da hanyoyin da kwamitin zai bi domin fara aiwatar da aikin nasa.
Wada Umar Rano ya ce biyu daga cikin matakai biyar din da kwamatin zai fara aiki a kansa ya hadar da gurfanar da wadanda aka kama da laifin satar yaran a gaban Kotu da kuma tashin tashar mota ta New Road dake sabon gari zuwa wani guri na daban.
Karin labarai:
Yaran Kano 9: Ganduje ya kafa kwamitin bincike na musamman
Kano9: Karanta cikakken labarin yaran Kano da aka sace
Justice Wada Umar Rano ya kara da cewa kwamatin ya gano cewa yaran da ake tunanin an sace ‘yan asalin jihar Kano daga shekarar 2010 zuwa shekarar da muke ciki ta 2019 sun kai su 113.
Ya kuma ce zuwa yanzu an bai wa iyayen yaran da aka sace naira miliyan guda kowannen su, da kuma kula da ilimin yaran tun daga Firamare zuwa Sakandire da kuma jami’a.
You must be logged in to post a comment Login