Labaran Kano
Fitar Zaki a Kano: Akwai bukatar duba na tsanaki kan gidan adana dabbobin daji
Bayan da rikakken zakin nan da ya kwace a gidan adana dabbobin daji na jihar Kano ya koma kejinsa bayan shafe awanni 40 ana fama da shi, masana da dama dai na bayyana cewa, akwai bukatar mahukunta jihar su yi duba na tsanaki kan gidan ta hanyar lalubo hanyoyin da za su kare aukuwar makamanciyar matsalar a gaba.
Daga cikin abinda masanan ke magana a kai sun hadar da samar da ingantattu kuma wadatattun kayan aikin kula da dabbobin, tare da kara yawan adadin abincin da ake ciyar da dabbobin.
A nazarin na masana dai, sun bayyana cewa, daga cikin matsalolin da gidan ke fuskanta akwai rashin isassun kayan aiki da ya sa har sai da aka nemo allurar da za ta kashe kuzarin zakin daga birnin tarayya Abuja, kasancewar babu ita a nan Kano, inda hakan ya baiwa zakin damar kwashe kusan kwanaki 2 ana fama da shi kafin ya koma kejin nasa.