Connect with us

Labaran Kano

 Za’a karrama Zakin da ya kufce daga gidan Zoo

Published

on

Wata kungiyar kare hakkin bil’adama a nan Kano ta shirya wani kasaitaccen bikin karrama murgujejen Zakin nan da ya kufce daga gidan Zoo a karshen makon da ya gabata.

Shugaban kungiyar Qaribullahi Yahya Lawal Kabara ya bayyana cewa zasu baiwa Zakin kyauta sakamakon yadda ya shafe tsawon wuni biyu amma bai yarda ya tozarta wani dan adam ba, sai ma kare ran dan adam da Zakin ya yi ta hanyar kin cutar da koda jariri.

Duk da cewa Zakin yayi sanadiyyar rasa ran ‘yan uwansa dabbobi, amma yayi hankali da bai cutar da ‘dan adam ba, don haka ya zama tilas su karrama shi.

Nan bada jimawa ba dai za’a sanar da ranar wannan shagalin biki na karrama Zakin.

RUBUTU MAI ALAKA:

Fitar Zaki a Kano: Akwai bukatar duba na tsanaki kan gidan adana dabbobin daji

Dalilin komawar Zaki gidan sa

Ganduje ya bada umarnin a harbe Zakin gidan Zoo

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!