Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Kano : An fara sauraron karar mutane 3 da ake zargi da laifin kisan kai

Published

on

Babbar kotun jiha mai zamanta a Miller Road karkashin jagorancin mai shari’a Aisha Mahmud Ibrahim, ta fara sauraron karar da aka gurfanar da wasu mutane uku a gabanta da ake tuhuma da laifin kisan kai.

Wadannan mutane sun hada da Aminu Malam da Martins Joseph da kuma Tahir Tanimu, dukkaninsu mazauna Unguwa Uku a nan Kano.

A ranar daya ga watan Maris din bara ne dai, aka zarge su da kashe wani matashi mai shekaru 18 Shamsu Yakubu, bayan sun caka masa wani makami a kirjinsa.

Laifin da ake zarginsu da aikatawa ya saba sashe na 221 na kundin Penal Code.

Wakilinmu na kotu Bashir Muhammad Inuwa ya rawaito cewa bayan karanta musu kunshin tuhumar sun musanta zargin, daga nan ne mai gabatar da kara kuma lauyan gwamnati Barista Lamido Abba Soron Dinki ya nemi kotu da ta dage sauraron karar zuwa wani lokaci.

Daga nan ne mai shari’a Aisha Mahmoud Ibrahim ta dage zaman shari’ar zuwa ranakun 17 da kuma 18 na watan Nuwamba mai zuwa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!