Labaran Kano
Kano: An karrama jami’an lafiya
Shugaban sashen lafiya na karamar hukumar Tofa Alhaji Adda’u Ubale Rano, ya yi kira ga dukkanin ma’aikatan lafiya dake karkashinsa da su kara zage dantse wajen maida hankali kan ayyukansu domin kara samun nasara a dukkan ayyukan da suka sanya a gaba.
Alhaji Adda’u Ubale Rano ya bayyana hakan ne yayin da yake mika kyautuka ga wasu daga cikin ma’aikatan wadanda suke bangaren bada allurar rigakafi bisa irin jajircewar da suka yi yayin gudanar da allurar rigakafin.
Ya kara da cewa, karamar hukumar Tofa ta dade a mataki na kasa a fannin alluran rigakafi amma bisa dagewar da ma’aikatan suka yi a wannan lokaci karamar hukumar ta dawo mataki na biyun farko a fadin jihar Kano.
A nata bangaren mataimakiyar Shugaban da ke lura da allurar rigakafin shiyyar Dawakin Tofa Hajiya Zullaiha Ahmad ta bayyana irin jajecewar da Adda’u Ranon ya yi wajen ganin karamar hukumar ta haura zuwa mataki na gaba da.
Wakilinmu Umar Lawan Tofa ya rawaito cewa a yayin taron Alhaji Abdu Umar da yawakilci Hakimin Tofa da sauran dagatai sun bayyana jin dadin su bisa nasarar da karamar hukumar ta samu ta zuwa mataki na gaba a bangaren kiwon lafiya.