Labarai
Kano: An yiwa malamai fince a kudin addu’ar Corona
Hukumar karbar korafe-korafe da yaki da rashawa ta Kano ta ce, ta kaddamar da bincike kan zargin zaftarewa malaman addini kudin addu’a da gwamna ya ba su a ranar arfa.
Shugaban hukumar Muhyi Magaji Rimin Gado ya shaidawa Freedom Radio cewa, sun samu korafi daga wasu malamai, kan zaftarar da aka yi musu, cikin kudin da gwamna ya basu, kuma tuni suka aika da sammaci ga bangarorin da abun ya shafa domin fadada bincike.
Wani Alaramma da abun ya shafa, ya shaidawa Freedom Radio cewa, an bashi dubu hamsin, amma dan gidan mai baiwa gwamna shawara kan al’amuran addinai Huzaifa Ali Baba ya karbe dubu arba’in da biyar daga hannunsa.
Freedom Radio ta tuntubi mai baiwa gwamna Ganduje shawara kan addinai Ali Baba Agama Lafiya Fagge, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin sannan ya ce, shi ne ya sanya ayi hakan domin a raba sauran ga ragowar malamai wadanda suka yi ta su addu’ar daga gida, duba da halin Corona da ake ciki.
Ali Baba ya kuma ce, shi da kansa ya raba wata rigimar kan wannan zaftare, tsakanin wasu malamai wadanda suka bi wasu har gida da makamai.
Sai dai kuma, gwamnatin Kano ta ce ba da saninta aka yi wannan zaftare ba, kamar yadda kwamishinan al’amuran addinai na Kano Malam Tahar Adamu Baba Impossible ya ce.
Yanzu haka dai, wannan batu na ci gaba da daukar hankalin jama’a, inda mutane da dama ke ta bayyana ra’ayoyinsu akai.
You must be logged in to post a comment Login