Labaran Kano
Kano: Ana zargin shugabannin makarantu da karbar kudi
Wasu daga cikin shugabannin makarantu a jihar Kano sun koka cewar har zuwa yanzu gwamnatin jihar Kano bata sakar musu isassun kudaden gudanarwa ba wanda za a yi amfani da su wajen tafiyar da tsarin bada ilimin Firamare da na Sakandire kyauta.
A kwanakin baya ne dai gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar tsarin na bada ilimi kyauta kuma tilas, sai dai an gano yadda wasu daga cikin shugabannin makarantu ke karbar kudade daga hannun iyaye sunan karbar kudin shaidar kamala makaranta da sauransu, kamar yadda wani magidanci da aka bukaci kudi a wurinsa ya kuma shaida wa Freedom Radio.
A baya dai wasu daga cikin shugabannin makarantu sun ce suna karbar irin wadannan kudade ne sakamakon rashin kudin gudanarwa da suke fama dashi, kasancewar gwamnati bata kai ga basu kudin gudanarwar da ta alkawarta ba.
Abubakar Muhammad Kidir sakataren ilimi ne na karamar hukumar Dala a nan Kano ya bayyana cewa, ya musanta cewa ana karbar kudi daga dalibai a karamar hukumar yana mai cewa, amma sun kafa kwamitin da zai gudanar da bincike kan zargin.
Haka kuma ya kara da cewa sun ja kunnen shugabannin makaratun karamar hukumar da, su kauracewa karbar kudi a hannun mutane, domin gwamnatin jihar Kano za ta rika basu kudaden gudanarwa.
A zantawar Freedom Radio da shugaban hukumar ilimin Firamare ta jihar Kano Dr Danlami Hayyo, ya ce har yanzu batun ilimi kyauta yana nan daram a jihar Kano, kuma za su gudanar da bincike kan kananan hukumomin jihar Kano 44 domin gano ko akwai masu karbar kudin tare da hukunta su.