Labarai
Kano: Ana zargin wani matashi da kashe Kakanninsa

Ana zargin wani matashi mai suna Mutawakkil wanda aka fi sani da Tony, da hallaka kakanninsa ta hanyar caka musu Wuka a unguwar Kofar Dawanau da ke yankin ƙaramar hukumar Dala.
Lamarin dai ya faru da safiyar yau Alhamis, inda ake zargin matashin ƴa yi amfani da wata Wuka ya sossoka musu, da kuma daga bisani ya yi ƙoƙarin guduwa ta hanyar haurawa wani gida.
Sai dai mazauna unguwar sun yi ƙoƙarin kama shi amma ba su samu nasara ba, wanda daga bisani suka gayyato jami’an Hisbah da su kuma suka shaida wa ƴan sandan ofishin Dala inda suka samu nasarar cafke shi.
Wakilinmu ya tuntuɓi jami’in hulɗa da jama’a na Rundunar ƴan sandan Kano Abdullahi Haruna Kiyawa, inda ya tabbatar da rasuwar mutanen, sai dai ya ce a jira shi zai yi ƙarin bayani a nan gaba.
You must be logged in to post a comment Login