Labaran Kano
Kano ba ta bukatar kafa rundunar tsaro -Ganduje
Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya ce, jihar ba ta bukatar kafa wata rundunar tsaro mallakin ta.
Gwamna Ganduje ya bayyana kuma jin dadin sa game da yadda jami’an tsaro ke gudanar da aikin su a jihar.
Wannan na cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan Kano Abba Anwar ya fitar jiya a nan Kano.
Sanarwar ta ce, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana hakan ne lokacin da sabon mataimakin Sufeto Janar na yan sanda shiyya ta daya AlG Sadik Abubakar Bello ya kai masa ziyara gidan gwamnati.
A cewar sanarwar, gwamnan na Kano ya nuna gamsuwar sa bisa yadda jami’an tsaro ke gudanar da ayyukan su na tsaron lafiya da dukiyar al’umma, kasancewar wanzuwar hadin kai tsakanin hukumomin tsaro.
Abdullahi Umar Ganduje ya kara da cewa, shakka babu jihar Kano na amfani da sababbin na’urori na zamani da za su taimaka wajen dakile ayyukan batagari.