Labarai
Kano da Jigawa: Hatsarin mota ya yi sanadiyyar mutuwar ƴan kasuwar Kano 9

An yi jana’izar ƴan kasuwa 9 na ƙaramar hukumar Gaya a nan Kano da suka rasa ransu jiya Litinin a wani hatsarin Mota.
Gidan Rediyon jihar Kano ya rawaito cewa, mutanen sun gamu da hatsarin ne a kan hanyarsu ta zuwa kasuwar Shuwarin a jihar Jigawa.
Rahotanni sun ce mutane 17 ne hatsarin ya rutsa da su, inda 9 daga ciki suka rasu nan take, mutane 8 kuma suka samu rauni.
You must be logged in to post a comment Login