Labarai
Kano: Dakarun Civil Defense sun kama wanda ake zargi da ayyukan Tsibbu da kuma damfarar kudi

Rundunar tsaro ta Civil Defense a Kano ta kama wani Dan Tsibbun Malami da take zargi da laifin damfarar wata mace sama da Miliyan daya da dubu dari Takwas da Talatin bayan ya binne mata wasu Manyan Layun daurin Baki a gidan ta domin neman sa’a.
Rundunar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta SC Ibrahim Idris Abdullahi ya fitar.
Ta cikin sanarwar SC Ibrahim ya ce, matashin yana karbar kudin matar ne da sunan zaiyi mata Addu’ar bunkasa harkokin kasuwancin ta da kuma inganta ilimin ‘ya ‘yanta.
Da ta ke jawabi kan yadda lamarin ya faru, matar mai suna Sa’adatu Abdu Auwal, ta ce, duk abinda ya yi mata daurin baki ne domin komai ya nema a wajen ta sai ta ba shi.
Shi ma wanda ake zargin Salisu Aliyu dan asalin Unguwar Kawo mazaunin garin Garko, ya ce tabbas ya karbi kudaden da nufin yi mata addu’a kamar yadda ya yi wa makobtanta taimako kuma suka ji dadi shi ya sa ita ma ta je neman sa a wajensa.
Rundunar ta ce, da zarar ta kammala duk wani bincike a kan wanda ake zargin za ta gurfanar da shi a gaban Kotu.
You must be logged in to post a comment Login