Kasuwanci
Kano: Direbobin Adaidaita Sahu sun yi karin farashin hawa babur
Kungiyar direbobin baburan adaidaita sahu ta Kano ta tabbatar da karin farashin kudin hawa babur din adaidaita sahu.
A cewar kungiyar karin farashin ya fara ne daga ranar talata kuma ya shafi dukkannin harkokin sifirin baburan adaidaita sahu a jihar Kano.
Shugaban kungiyar Alhaji Mansur Tanimu Dankoli ne ya tabbatar da hakan lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a ranar litinin.
A cewar sa daukar matakin karin ya faru ne sakamakon ci gaba da samun tsadar rayuwa musamman na karin farashin wasu kayayyakin da suke amfani dasu.
‘‘Inda ake biyan naira 30 yanzu ya zama 50, gurin 70 kuma dawo naira 100 yayin da wajen da a baya ake dauka akan 100 yanzu ya dawo 130 zuwa 150, na 180 shi kuma ya dawo 200 yayin da na 200 ya karu zuwa naira 250’’ a cewar sa.
A nasa bangaren Halliru Shap -Shap wanda shine mai wayar da kan jama’a akan karin farashin da kungiyar tayi, ya ce, wajibi ne kungiyar ta yi karin a wannan lokaci sakamakon tsadar rayuwa da ake fama da ita.
You must be logged in to post a comment Login