Labarai
Kano: Jami’an Civil Defence sun cafke kayan da suke zargin an sato
Hukumar tsaro ta Civil Defense shiyyar Kano, ta ce, samu nasarar gano tarin wasu kayayyakin da take zargin na sata ne da suka hada da Atamfofi da Lesuna da Shaddoji da Huluna har ma da Talabijin ta bango.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar SC Ibrahim Idris Abdullahi, ne ya bayyana hakan ga Freedom Radio ya na mai cewa lamarin ya faru ne da yammacin ranar Talata.
Ya ce, jami’an sun samu nasarar ne a kan babban Titin zuwa Gwarzo da ke a tsakanin unguwannin Rijiyar Zaki da Ɗanbare.
A cewarsa jami’an su dake gudanar da bincike ne suka gano kayayyakin da suke zargin na satar ne a inda suka yi kokarin tsayar da diraben Adaidaita Sahun daya dakko wata mace dauke da kayan amma sai suka tsere suka bar kayan a cikin Adaidaita Sahun.
Mai magana da yawun rundunar SC Ibrahim Idris Abdullahi ya kuma yi kira ga al’umma musamman wadanda suka san an yi musu sata a baya-bayan nan dasu garzaya zuwa shalkwatar rundunar ta Civil Defense ta Kano domin su duba kayan.
Rahoton: Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa
You must be logged in to post a comment Login