Labaran Kano
Kano – Kotu ta aike da matashi gidan gyaran hali bisa laifin kisa
Kotun majistire mai lamba 42 karkashin mai shari’a Hanif Sanusi Yusuf, ta aike da wani matashi mai suna Auwal Abdullahi Ayagi gidan gyaran hali, bisa zarginsa da laifin kisan kai.
Kunshin tuhumar da ‘yan sanda suke masa ya bayyana cewar a ranar 27 ga watan Agustan da ya gabata, an samu rashin fahimta tsakanin Auwal Abdullahi Ayagi da Umar Garba a kan kofin shayi, har kuma Auwal Ayagi ya cakawa Umar Garba wuka a kirji, kuma nan take rai ya yi halinsa.
Yayin da aka karanta masa tuhumar, Auwal Aayagi ya amsa cewar tabbas wannan zargi babu kokonto, domin ya aikata laifin, ko da yake ya ce sharrin shaidan ne.
Kotun ta yi umarnin da a ajiye shi a gidan gyaran hali zuwa ranar 29 ga watan satumbar nan da muke ciki, an kuma umarci ‘yan sanda da su gabatar da kundin bincike domin lauyoyin gwamnati su fadada bincike.
Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il ya ruwaito cewa laifin ya saba da sashi na 221 na kundin hukunta manyan laifuka.
You must be logged in to post a comment Login