Labarai
Kano: Kotu ta amince da buƙatar Malam Abduljabbar na janye ƙarar da ya kai Gwamna Ganduje
Babbar kotun tarayya da ke Gyaɗi-gyaɗi a Kano ta ci gaba da sauraron ƙarar da Malam Abduljabbar Kabara ya shigar kan matakin da Gwamnati ta ɗauka a kansa.
Malam Abduljabbar ya yi ƙarar Gwamnan Kano, Atoni Janar na jiha da Kwamishinan ƴan sanda da hukumar tsaron farin kaya da hukumar tsaron Civil Defense.
Yayin zaman kotun na yau Alhamis, wasu lauyoyi daga ƙungiyoyin Tijjaniyya Movement Initiative da Islamic Forum of Nigeria da kuma Jama’atu Tajdidil Islam sun sun nemi a sanya su cikin ƙunshin waɗanda malamin yake ƙara.
Sai dai lauyan Sheikh Abduljabbar Barista Saleh Muhammad Bakaro ya nemi iznin kotun domin ya janye ƙarar.
A ƙarshe mai shari’a Lewis Alagua ya amince, tare da soke shari’ar nan take.
Hakan na zuwa ne kwana guda bayan da malamin ya aike da wani saƙon fefen bidiyo da a ciki ya roƙi lauyoyin sa su janye shari’ar.
You must be logged in to post a comment Login