Labarai
Kano: Lauyoyi sun yi barazanar gurfanar da kwamishinan ‘yan sanda
Kano: Lauyoyi sun yi barazanar gurfanar da kwamishinan ‘yan sanda
Kungiyoyin kishin alumma karkashin Barrister Abba Hikima sun yi barazanar gurfanar da kwamshinan ‘yan sandan Kano a gaban kotu bisa zargin da ‘yan uwan wani matashi suka yi na jami’an ‘yan sandan SARS sun azabtar dashi har takai ya rasu.
Yan uwan dai sun garzaya kotu suna neman a bi musu hakkin su kan kisan gillar da aka yiwa dan uwansu, babu gaira babu sabar.
Idan dai baku manta ba a kwanakin baya ne wasu mata da suka bayyana cewar an zargi dan uwansu Mustapha Idris Muhd da laifin sata, amma da aka tashi sai aka kaishi sansanin yaki da ‘yan fashi da makami wato SARS.
A kuma sashen ne a cewar dangin jami’an suka dinga jibgarsa har sai da yayi laga-laga, daga bisani kuma Allah yayi masa rasuwa.
Rahotanni sun bayyana cewar, dangin sun yi kukan cewar bayan rasuwar tasa ma ba a sanar dasu ba sai bayan kwanaki sama da 10 sannan ne aka sanar dasu suje su dauki gawar, kuma koda suka zo yi masa wanka sun ga ikon Allah domin ilahirin jikinsa duka ne da wani abu kamar ma kunar wuta.
Amma da muka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya musanta zargin yana mai cewar dan uwan mamacin ba’a hannun su ya rasu ba, hasali ma asibiti ne ba kamar yadda suke ikirari ba.