Labarai
Kano: Ma’aikatar Muhalli ta haramta wa kamfanoni karya dokar aikin tsafta

Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi ta jihar Kano ta sanar da soke duk wata dama da aka bai wa kamfanoni na yin aiki a ranar da ake gudanar da aikin duben tsaftar muhallin a duk ƙarshen wata.
Kwamishinan ma’aikatar, Dakta Dahiru Muhammad Hashim, ne ya bayyana hakan a yau Alhamis.
Kwamishinan, ya ɗauki matakin ne bayan karɓar wani rahoto da ke nuna cewa wasu kamfanoni su na karya dokar ta hanyar yin zirga-zirga a lokacin aikin tsaftar.
Haka kuma, ya ce, ma’aikatar ba za ta lamunci hakan ba kuma za ta dauki mata kan duk wanda ta samu da karya dokar.
You must be logged in to post a comment Login