Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Doka za ta yi aiki kan masu karya dokar tsaftar muhalli- Dr Getso

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta bukaci hadin kan al’ummar jihar don ganin sun bada gudunmawa wajen tsaftace muhallan su da kasuwanni a karshen kowanne wata.

Kwamishinan muhalli na jihar Kano Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya bayyana hakan, lokacin da yake ganawa da kwamitin kar-ta-kwana na tsaftar muhalli.

Hakan na cikin wata sanarwar da jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar Abbas Habeeb Abbas ya sanyawa hannu.

Ya ce, a gobe Juma’a ne za a gudanar da tsaftar kasuwanne kamar yadda aka saba a karshen kowanne wata daga karfe bakwai na safe zuwa goma, yana mai cewa akwai bukatar ‘yan kasuwa su bada hadin kai wajen tsaftace kasuwannin su.

Kazalika sanarwar ta bayyana cewa, ranar asabar zai kasance ranar tsaftar muhalli na duk gari a don haka ma’aikatar ta gargadi masu karya doka a yayin da ake gudanar da aikin da su guji fitowa don kuwa doka zata hukunta masu yi mata karan tsaye.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!