Labarai
Kano: Majalisar wakilai ta nemi a rushe ƴan sandan ‘Anti Daba’
Majalisar wakilan ƙasar nan ta nemi a rushe sashen ƴan sanda mai yaƙi da ƴan daba na ƴan sandan Kano wato Anti Daba.
Shugaban kwamitin tsaro na majalisar Sha’aban Ibrahim Sharaɗa ne ya nemi hakan yayin da ya ziyarci kwamishinan ƴan sandan Kano.
Sha’aban Sharaɗa ya je wurin kwamishinan ne kan zargin wasu jami’an ƴan sandan Anti Daban da hallaka wasu matasa biyu a unguwar Sharaɗa.
Labarai masu alaka:
Ƴan sanda sun musanta yin kisan kai a Kano
Kano: Ƴan sanda sun cafke mai buga jabun takardun ɗaukar aiki
Ƴan sanda sun tabbatar da kisan mutane biyu a Sharaɗa
Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta cafke ƴan sandan sashen Anti Daba da suka je sumame unguwar Sharaɗa.
Ana zargin jami’an da yin sanadiyyar rasa ran matasa biyu a daren Asabar.
Jami’in hulɗa da jama’a na ƴan sandan Kano DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ya shaida wa Freedom Radio hakan.
Ya ce, “yanzu haka su na tsare a shalkwatar ƴan sanda da ke Bompai domin ci gaba da bincike”.
You must be logged in to post a comment Login