Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Addini

Kano: Malamai sun nemi a rage yawaita buɗe masallatai

Published

on

Majalisar Malamai ta ƙasa reshen jihar Kano ta yi kira ga al’umma kan a rage yawaita buɗe masallatai domin magance rabuwar kan musulmi.

Majalisar ta bayanna hakan ne, a jawabinta na bayan taron bitar kwanaki da ta shiryawa limaman Kano da haɗin gwiwar sashen nazarin addinin musulunci na jami’ar Bayero.

Mataimakin Babban Sakataren Zauren Farfesa Muhammad Babangida Muhammad ne ya aike wa da Freedom Radio jawabin bayan kammala taron a ranar Lahadi.

Jawabin ya umarci limamai da su raya masallatan da ake da su ta hanyar salloli da lakcoci da kuma karatukan zaure.
Sannan majalisar ta ƙarfafi limamai kan su riƙa ziyartar junansu domin sada zumunta.

Majalisar malaman ta kuma umarci limamai da su yawaita yiwa masu mulki a kowane mataki nasiha, dangane da nauyin da yake kansu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!