Labarai
Kano: Masu faɗan Daba sun hallaka wani matashi Dorayi

Wasu masu faɗan daba sun hallaka matashi Yusuf Ahmad a unguwar Dorayi da ke Kano.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya tabbatar da mutuwar matashin a wani bidiyon kai tsaye da ya yi daga unguwar ta Dorayi kan lamarin.
Kiyawa ya bayyana cewa, rundunar ta samu kiran gaggawa kan faɗan, inda Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya bayar da umarnin tura jami’ai zuwa wurin.
Ya ce, bayanan farko sun nuna cewa wasu matasa sun yi wa ɗan wani tsallake a unguwar rauni, abin da ya fusata ’yan yankinsa, inda su ma suka yo gayya suka fito.
Ya ƙara da cewa, ’yan sanda sun kai ɗauki tare da kama wasu da ake zargi da hannu a lamarin.
Wani mazaunin yankin, Salihu Shamsu Saleh, ya bayyana cewa Yusuf ya je maulidin makarantarsu tsallaken, kuma a kan hanyarsa ne masu faɗan dabar suka afka masa, inda ya ce an sare shi a ƙirji da wuya.
Kiyawa ya jaddada cewa, ana ci gaba da bincike domin gano sauran waɗanda ake zargi da hannu a lamarin.
You must be logged in to post a comment Login