Labarai
Neja: Yan Sanda sun kama mutane 5 da ake zargi da haɗa kai wajen aikata fashi

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja ta kama mutane 5 da ake zargi da haɗa baki wajen aikata fashi da makami a wasu yankunan Minna, tare da kwato ƙaramar bindiga ƙirar Barretta guda ɗaya da harsasai biyu.
Hakan na cikin sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar, SP Wasiu Abiodun, ya fitar aka rabawa manema labarai.
Ya ce, lamarin ya faru ne ranar 11 ga Agusta 2026, bayan wasu masu fashi da makami sun shiga gidaje a yankin Sauka Kahuta da ke Minna, inda suka sace kwamfutoci, wayoyi, babura da sauran kayayyaki.
Sanarwar ta ce, binciken ’yan sandan ya kai ga kama jagoran ƙungiyar, wanda daga bisani ya taimaka wajen kama sauran mutum uku da ake zargi da hannu a hare haren fashi da aka yi a wasu yankunan Minna.
Rundunar ta ce daga baya ta kama mutum na biyar da ake zargi da ajiye musu bindiga, inda aka kwato bindigar Barretta mai harsasai 2.
You must be logged in to post a comment Login