Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kano ta bai wa Ma’aikata hutun ranar Takutaha

Published

on

Gwamnatin jihar Kano, ta sanar da ranar Talata 1 ga watan Satumban bana a matsayin ranar hutu domin bai wa al’ummar Musulmi damar yin bikin zagayowar ranar sunan Ma’aiki watau Takutaha da ake gudanarwa a duk shekara.

 

Gwamnatin ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanrwa da ta fitar mai dauke da sa hannun babban sakataren Abba A. Danguguwa a madadin shugabar ma’aikata.

 

Ta cikin sanarwar, gwamnatin ta bayyana cewa, gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da bayar da hutun ne la’akari da irin muhimmanci da kuma girman Takutaha ga mutanenn Kano ta fuskar addini da kuma al’adu.

 

Haka kuma, ta cikin sanarwar, gwamantin ta bukaci ma’aikata har ma da sauran al’umma da su yi amfani da lokacin wajen gudanar da addu’o’i musamman ma wajen samun tsaro da kuma hadin kai a tsakanin al’ummar Kano da ma na fadin kasar nan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!