Labaran Wasanni
Kano Pillars ta lallasa Delta Force da ci 6-1
Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta koma mataki na 10 a teburin gasar Firimiyar Nigeria, bayan da ta buga wasan makon na 7 na kakar wasanni ta bana.
Hakan ya biyo bayan lallasa Delta Force da ta yi da ci 6 da 1, a wasan da aka fafata a filin wasa na Sani Abacha dake Kofar Mata a birnin Kano.
Dan wasan Kano Pillars David Ebuka ne ya fara zura Kwallo a minti 3 da fara wasan, yayin da Abdullahi da Auwalu Ali Malam suka kara kwallaye a mintuna 22 da 53.
Dan wasan Delta Force Bala Yahuza , shine ya rama wa Delta Force, Kwallo daya tilo a Minti 57, kafin daga bisani Rabiu Ali da Chijioke Aleakwe, suka karawa Pillars kwallaye a mintuna 60 da 66 da 86, inda aka tashi daga wasa Kano Pillars na da ci 6 Delta Force na da 1.
An zabi Jagoran yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars Kyaftin Rabiu Ali a matsayin gwarzon dan wasa.
Da yake zantawa da manema labarai Kyaftin Rabiu Ali ya ce, yanzu haka kungiyar ta dawo da karsashin ta, inda ya kara da cewa sun shirya tsaf don samun nasara a dukkanin wasannin da zasu fafata.
A nasa bangaren mai horar da ‘yan wasan kungiyar ta Kano Pillars Ibrahim Musa Jugunu, yace kungiyar ta dogara ne da addu’oin dumbin magoya baya da kuma, kokarin ‘yan wasan tare da irin rawar da jagororin kungiyar ke takawa.
Wakilinmu Aminu Halilu Tudunwada, ya ruwaito cewa wannan shi ne karo na farko a gasar firimiya ta bana da kungiyar ta Pillars ta yi wasa dan ‘yan kallo, bayan da a baya aka dakatar dasu shiga na wasanni uku sakamakon samun su da aikata ba dai dai ba.