Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Kano Pillars ta sabunta kwantiragin Jugunu na shekara daya

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, ta tsawaita kwantiragin mai horar da ‘yan wasan ta Ibrahim Musa da aka fi sani da Jugunu, na shekara daya zuwa kakar wasanni na gaba 2020/2021.

A cewar shugaban kungiyar Alhaji Surajo Yahaya Jambul, ta hannun kakakin kungiyar Rilwanu Idris Malikawa Garu, an sabunta kwantiragin Jugunu ne sakamakon kwazon sa a baya.

Alhaji Surajo Jambul, ya umarci mai horarwar da yayi aiki tare da mataimakan sa, ‘yan wasa da daukacin ma’aikatan kungiyar don samun nasara a kakar badi.

Ya kuma yi alkawarin, rubanya walwalar ‘yan wasan tare da aiki da duk masu ruwa da tsaki don bunkasa kungiyar zuwa matakin ci gaba.

Da yake jawabi, bayan saka hannu a kwantiragin, Ibrahim Musa Jugunu, ya sha alwashin biyan bashin amincewa da tawagar tayi dashi wajen samarwa da kungiyar nasarori.

Kungiyar ta Kano Pillars, na shirye-shiryen tunkarar kakar wasannin badi, a bangarori uku ,na gasar Firimiya ta kasa sai gasar kofin kalubale na Aiteo Cup da na nahiyar Afirka na CAF Confederation cup.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!