Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Wasanni: Shekarau Babes FC za ta buga gasar rukuni na daya na NNL

Published

on

Tawagar Shekarau Babes FC, ta tabbatar da cewar zata shiga a dama da ita a gasar rukuni na daya wato Nigeria National league (NNL), na kakar 2021/2022.

Mai kungiyar, tsohon Gwamnan jihar Kano kuma sanatan Kano ta tsakiya Malam Ibrahim Shekarau ne, ya bayyana haka a daren Juma’a lokacin da ya tattauna da mukarraban kungiyar a birnin tarayya Abuja

Malam Ibrahim Shekarau, ya shawarci mukarraban da su zakulo matasan ‘yan wasa masu hazaka don wakiltar kungiyar yadda ya kamata, sannan ya yi alkawarin cewar da zarar an samu hazikai 5 a cikin su, zai dau nauyin fitar da su zuwa kasashen ketare don samun kungiyoyin kasashen waje.

A sanarwar da kakakin tawagar Ahmad Babandi Gama, ya sakawa hannu wadda aka rabawa manema labarai, Malam Shekarau ya ce, kowa ya san muhimmancin da harkokin wasanni yake dashi wajen bunkasa matasa da samar musu da ayyukan yi, don haka a shirye yake a koda yaushe don bada gudummawa a bangaren.

Sanatan na Kano ta tsakiya ya godewa jagororin kungiyar da ‘yan wasa, duba da lokacin su da himma da suke bayarwa a kan kungiyar a koda yaushe ba tare da gazawa ba, tare da umartar su kan su zama jakadu nagari a koda yaushe.

*AHT*

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!