Labaran Wasanni
Kano Pillars ta samu nasara karon farko a kakar wasanni ta bana

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta samu nasarar doke takwararta ta Akwa Starlet da ci biyu da daya a wasan mako na shida na gasar Firimiya ta kasa.
Nwagua Nyima shine ya zurawa Pillars wannan kwalleye biyu a minti 27 da minti 79, yayin da Moses Effiong ya zurawa Akwa Startet kwallonta daya tilo.
Wannan dai shine karo na farko da Kano Pillars ta samu nasara a gasar Firimiya ta kasa a kakar wasanni ta bana.
Yanzu haka dai Kano Pillars tana mataki na sha biyar a teburin da maki shida, biyo bayan buga wasanni shida.
A wasanni shida da Pillars ta fafata ta yi nasara a wasa daya, rashin nasara a wasanni biyu, sai canjasaras a wasanni uku.
A ranar lahadi mai zuwa Pillars zata buga wasan mako na bakwai da Delta Force a filin wasa na Sani Abatcha dake Kofar mata a Kano.