Connect with us

Labarai

Zaɓen ƙananan hukumomi ya fi kama da wasan kwaikwayo – PDP tsagin Kwankwaso

Published

on

Jam’iyyar PDP tsagin tsohon Gwamna Kwankwaso ta ce, zaɓen ƙananan hukumomi da aka yi a Kano wasan kwaikwayo ne.

Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar Bashir Sanata ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙon bidiyo da ya fitar a shafinsa na Facebook wanda ya karaɗe kafafen sada zumunta.

Sanata ya ce, suna godiya ga ƴan jam’iyyarsu bisa bin umarnin da suka bayar na a ƙauracewa zaɓen.

A cewar sa, rashin fitowar jama’a a zaɓen na nuna cewa al’ummar Kano na tare da su ɗari bisa ɗari.

Karin labarai:

An cafke Budurwa mai garkuwa da mutane a Kano

Kano: Yawan ƙuri’un zaɓen ƙananan hukumomi sun zarce na zaɓen Gwamnan 2019

Sai dai tuni ɓangaren Aminu Wali na jam’iyyar ta PDP suka ce, sun shiga kuma an kara da su a zaɓen, yanzu haka ma sun shiga tattara bayanai domin ɗaukar mataki na gaba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,482 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!