Labarai
Kano: Za a gwada ƙwaƙwalwar matar da ake zargi da hallaka ƴaƴanta

Kotun majistiri mai lamba biyar da ke gidan Murtala ƙarƙashin mai shari’a Hauwa Lawan Minjibir ta fara sauraron shari’ar matar da ake zargi da hallaka ƴaƴanta.
A yayin zaman shari’ar na ranar Talata lauyan gwamnati Barista Lamiɗo Abba Soronɗinki ya karanto mata tuhumar da ake mata.
Ana zargin matar ne da hallaka ƴaƴanta biyu a watan Oktoban da ya gabata, a ƙaramar hukumar Gwale zargin da Hauwa’un ta musanta.
Lauyar wadda ake zargi Barista Huwaila Muhammad Ibrahim ta nemi kotu ta amince a kai wadda ake zargin asibiti domin duba ƙwaƙwalwarta.
Kotun ta amince da buƙatar, inda ta sanya ranar 5 ga watan Janairu na shekara mai zuwa domin ci gaba da shari’ar.
You must be logged in to post a comment Login