Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Kano9: Al’umma suna ta karrama kwamishinan ‘yan sanda sakamakon ceto yaran Kano

Published

on

Biyo bayan nasarar da rundunar ‘yansanda ta jihar Kano ta samu na ceto wasu kananan yara ‘yan jihar da aka sace kuma aka siyar dasu a can garin Onitsha, al’umma da dama suna ta tururuwa zuwa hukumar ‘yansanda domin jinjina mata kan wannan namijin kokari da tayi.

Izuwa yanzu dai kwamishinan ‘yansanda na jihar Kano CP. Ahmed Iliyasu ya samu karramawa da dama daga al’umma daban-daban na ciki da wajen jihar Kano.

Kalli hotunan wasu ziyarorin da aka kaiwa kwamishinan ‘yansanda na jihar Kano.

kungiyar tallafawa kananan yara.

kungiyar matasan Yarbawa.


Yayin da magajin garin Daura ya kawo ziyara ga kwamishinan.

Al’ummar Garin Wudil, Jagoranchin Makaman Kano kuma Hakimin Wudil Alhaji Sarki Abdullahi Ibrahim

Yayin ziyarar da Zauren Malaman Kano suka kawowa kwamishinan ‘yansanda

Kungiyar mata ‘yan jarida ta jihar Kano

Tawagar mai shinkafa na jam’iyyar APC da jama’arsa.

A yau jumu’a ne dai gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya kafa kwamiti na musamman da zaibi diddigi kan batun gano yaran da ma  sauran yara da iyayensu sukayi korafi amma ba’a kai ga gano su ba.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!