Labarai
Karɓar katin zaɓe wajibi ne ga duk ɗan ƙasa nagari – Falakin Shinkafi
Sponsored
Ambasadan zaman lafiya kuma Falakin Shinkafi Alhaji Yunusa Yusuf Hamza ya yi kira ga al’ummar Arewacin ƙasar nan da su tabbatar sun mallaki katin zaɓe domin samar da shugabanni nagari.
Falakin Shinkafi ya bayyana hakan ne, yayin zantawarsa da manema labarai.
A cewarsa katin zaɓe shi ne babban abin da talaka zai yi riƙo da shi, domin zaɓar shugabannin da zasu inganta rayuwarsa ta hanyar magance matsalolin tsaro da haɓaka tattalin arziƙi, tare da samar da abubuwan more rayuwa a birane da karkara.
”Bai kamata a ce wanda ya kai shekaru 18 a duniya ya zauna ba shi da katin zaɓe ba, duba da muhimmancin da yake da shi ga rayuwar al’umma” a cewarsa.
Ambasada Yunusa Hamza yace, karɓar katin zaɓe wajibi ne, haka shi ma yin zaɓen wajibi ne, don haka ya ƙalubalanci masu cewa ba zasu yi katin ba, saboda idan sun zaɓi shugabanni ba a ba su ko da sun lashe zaɓen.
Ya ce ”Da yin zaɓen ku bashi da amfani da Gwamnatin bata kashe maƙudan kuɗaɗe wajen shirya zaɓen ba, kuma da su kansu ƴan siyasar ba su zo wajenku nemen goyon baya ba, don haka waccan maganar bata da tushe balantana makama”.
Falakin na Shinkafi ya kuma yi kira ga shugabanni da sauran masu ruwa da tsaki kan su fito da wani tsari domin wayar da kan jama’a da sake basu dama tare da sauƙaƙa musu hanyar mallakar katin zaɓen cikin sauƙi.
LABARAI MASU ALAƘA:
Barka da Sallah daga Jarman Matasan Arewa Amb. Yunusa Hamza
An naɗa Ambasada Yunusa Hamza a matsayin Falakin Shinkafi
Ambasada Yunusa Hamza:
Ɗaya ne daga cikin jagororin matasa a arewacin Najeriya wanda yayi fice wajen gina rayuwar matasa, ta hanyar koyar da su sana’o’in dogaro da kai, tare da tallafa musu wajen neman ilimi.
Yana cikin zaƙaƙuran matasan Arewa da suka yi fice wajen shigewa gaba domin kare muradan al’ummar yankin.
You must be logged in to post a comment Login