Labarai
Karancin abinci da wutar lankarki ya janyo na sauke ministoci na – Buhari
Fadar shugaban ƙasa ta ce, kafin shugaba Buhari ya sauke ministocin sa biyu sai da yayi la’akari da yadda ƙasar ke fuskantar ƙarancin abinci da kuma hasken lantarki.
Mai bai wa shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai Femi Adesina ne ya sanar da hakan yayin zantawar sa da gidan talabijin na Channels.
Ya ce, samar da abinci da gyaran harkokin wutar lantarki muhimman abubuwa ne da shugaba Buhari ya sanya su a gaba, don samarwa da al’umma walwala.
Adesina ya kuma ce, ministocin da aka sauyawa wajen aiki ba su da rauni a tsoffin ofisoshin su, wannan ne ya sanya aka tura su zuwa muhimman ma’aikatun biyu.
A Larabar nan ne Buhari ya kori ministan Noma da raya karkara Muhammad Sabo Nanono da ministan lantarki Sale Mamman.
You must be logged in to post a comment Login