Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Buhari ya gaza cika alƙawuran da ya ɗaukarwa ƴan Najeriya – Majalisar Dokokin Katsina

Published

on

Majalisar dokokin jihar Katsina ta zargi gwamnatin tarayya da gazawa wajen cika alƙawarin da ta ɗaukarwa ƴan Najeriya na magance musu matsalolin su.

Dan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Danmusa Aminu Garba ne ya bayyana hakan, ta cikin wani faifan bidiyo da jaridar Premium times ta nazarta.

Ya ce, tuni gwamnatin shugaba Buhari ta sauka daga gwadaben da ta yi alƙawari, musamman na tabbatar da tsaro da kuma bunkasa tattalin arziki.

Aminu Garba ya bayyana hakan ne daidai lokacin da al’amuran tsaro ke ƙara ta’azzara a jihar Katsina.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!