Labarai
Karancin fitowar masu zabe abun tsoro ne- Abdulrazak Alkali
Kungiyar karfafawa mutane gwiwa don shiga harkokin dimokradiyya ta jihar Kano tace dimokuradiyya diyya a Najeriya na fuskantar barazana musamman a hannun kowacce jam’iyya mai mulki wanda hakan ke nuna Demokaradiyya a kasar nan bata samu gindin zama ba.
Shugaban kungiyar karfafawa mutane guiwa da shiga harkokin dimokuradiyya ta jihar Kano Kwamared Abdularak Alkali ne ya bayyana hakan ta cikin shirin muleka Mugano na musamman na gidan Radio Freedom a jiya Lahadi daya mayar da hankali kan zaben cike gurbi da aka gudanar a ranar Asabar data gabata.
Kwamared Abdulrazak Alkali ya kara da cewa matukar mutane suka fara yanke tsammanin samun Adalci a zabukan da ake gudanarwa shakka babu, abun ba zai haifar da da mai ido ba duba da irin kura-kuran da jam’iyyun ke tafkawa a lokacin zabe domin ganin ganin Jam’iyyarsu tayi nasara.
Abdulaziz Alkali yace zaben cike gurbi da akayi a ranar Asabar data gabata abun tsoro ne yadda aka samu karancin fitowar jama’a a wasu gurare sakamakon tsoron abunda kaje yazo na tashin hankali musamman yadda jagororin siyasa ke zuwa guraren zabe domin ganin jam’iyyarsu tayi nasara ta ko wane hali.
Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa ya ruwaito Shugaban kungiyar Kwamared Abdulaziz Alkali na cewa abun takaici ne yadda wasu kasashe suka ki amincewa da tura jami’an su masu sanya ido akan zabuka musamman a wannan zaben cike gurbi da ka gudanar a ranar Asabar data gabata sakamakon rashin ingantacciyar demokradiyyar kasar nan.