Labarai
Karancin kudi ya sanya ciyo bashi a kano-Majalisa
Majalisar dokokin Jihar kano ta ce, ta sahalewa gwamnatin Jihar karbo bashin billiyan Hamsin ne la’akari da rashin kudi da jihar take fama da shi, kuma sun sahale ne cikin gaggawa saboda hutun da majalisa za ta tafi a wancan lokaci, a wani mataki na kare kai daga cutar Corona.
Dan majalisar mai wakiltan Bunkure, kuma shugaban kwamitin kudi na majalisa Muhammad Uba Gujjiya ne ya bayyana hakan a yau, ta cikin shirin Barka da Hantsi na nan gidan Radio Freedom.
Muhammad Uba Gujjiya ya kuma ce, duba da cewa Jihar na da bukatar kudi kuma Jihohi da dama sun karbo, yasa majalisar ta sahalewa gwanman don karbo bashin wadancan kudaden.
Yana mai cewa, gwamnatin jihar Kano za ta yi amfani da kudaden ne wajen kammala ayyukan da ba a gama ba, da kuma inganta bangaren lafiya da kuma kara samar da ayyukan raya kasa.
Muhammad Uba Gujjiya ya bayyana cewa, ana sa ran za a biya wancan bashin cikin shekaru goma masu zuwa.
You must be logged in to post a comment Login