Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Karanta jawabin shugaban kan ranar samun ‘yan cin kai

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ba da umarnin fitar da naira biliyan dari shida cikin watanni uku masu zuwa, domin gudanar da ayyukan raya kasa, a sassa daban-daban na kasar nan.

Muhammadu Buhari ya bayyana hakan ne yayin da ya ke gabatar da jawabi ga al’ummar kasar nan, domin murnar cikar ta, shekaru hamsin da tara da samun ‘yancin kai daga turawan Burtaniya.

Shugaban kasar wanda ya fara jawabin da jinjinawa al’ummar kasar nan sakamakon jajircewar da ya ce, sun yi ,wajen tabbatar zamanta a matsayin dunkulalliya, ya ce gwamnatin sa, ta sauya wanda zai rika kula da shirin yaki da fatara da samar da aikin yi wato Social Investment Program.

A cewar Muhammadu Buhari, ba kamar yadda ya ke a baya ba, inda ofishin mataimakin shugaban kasa ke kula da shirin na social Investment program, a wannan karon, sabuwar ma’aikatar jinkan al’umma da takaita illar da ibtila’i’ kan haifar da kuma ci gaban al’umma, ita ce za ta rika kula da shirin

Ya ce shirin wanda aka ware naira biliyan dari biyar, ya hadar da: ciyar da yara ‘yan makaranta da shirin samar da aikin yi na ‘Npower’ da ba da bashi ga kananan masu sana’oi da kuma shirin samar da gidaje masu saukin kudi.

Haka zalika shugaba Buhari ya kuma ce gwamnatin sa, za ta bai wa harkokin Ilimi da lafiya da samar da ruwan sha da tsaftar muhalli da kuma tsaro fifiko a zangon mulkin sa na biyu.

Muhammadu Buhari ya ci gaba da cewa, aikata laifuka ta Internet ya zama wata babbar barazana ga daurewar kasar nan, sakamakon  yadda ake amfani da kafar wajen yada kalanaman tunzura jama’a, saboda da haka, gwamnatin sa za ta yi duk me yiwuwa wajen ganin ta dakile matsalar.

Shugaban kasar bai kammala jawabin sa ba, sai da ya kuma jaddada cewa, za su rika bibiyar ayyuka da tsare-tsare da su ke aiwatarwa da nufin nazartar nasarori da aka samu ko akasin haka, wadda hakan wata dabara ce, ta dakile me yiwuwar illar da hakan ka iya haifarwa ga talakawar kasar nan.

A ranar daya ga watan Oktoba, a alif da dari tara da sittin ne dai NAJERIYA, ta samu ‘yancin kai daga turawan Burtaniya.

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!