ilimi
Karin kudin makarantun Jami’o’i barazana ce ga harkokin tsaro: SEDSAC
- Mata sa zasu iya shiga matsala sakamakon karin kudin makaranta.
- Da gwamnatin tarayya tasan matsalar da karin kudin nan zai jawowa kasar nan da bata yi buris da bukatun ASUU ba.
- Kafin a kara kudin makarantar ma wasu daliban basa iya biyan kudin makarantar.
Wani mai fashin baki kan al’amuran yau da kullum dake jihar Kano, kuma shugaban kungiyar SEDSAC mai rajin habbaka harkokin ilimi kwamred Umar Hamisu Kofar Na’isa ya ce, karin kudin makarantar da jami’o’i suka yi ba karamar barazana zai haifarwa kasar nan ba, musamman a bangaren matasa.
Kwamred Umar Hamisu Kofar Na’isa ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da wakiliyar Freedom Radio Shamsiyya Farouk Bello.
Wanda yace ‘da gwamnatin tarayya tasan irin illar da karin kudin makarantar nan zai jawowa daliban kasar nan, da bata ki biyawa malaman jami’o’i bukatunsu ba’.
Kwamret Umar Hamisu Kofar Na’isa ya kara da cewa ‘ tun kafin a kara kudin makarantun jami’a, wasu daliban basa iya biyan kudin makarantar, wanda karinsa a yanzu zai kara sawa matasan kasa cigaba da karatun’.
A hannu guda shugaban kungiyar malaman Jami’o’i na Jihar Kano Farfesa Abdulkadir Muhammad cewa yayi ‘wannan matsalar na daya daga ciki abubuwan da malaman jami’a suka guda, wanda ya haddasa musu tafiya yajin aikin da sukayi na tsayin watanni takwas’.
Farfesa Abdulkadir Muhammad ya kuma ce ‘wannan ‘yan kare karen da akayi a yanzu ma ba komai bane fyace kudin irin nasu jarabawa dana magunguna da sauran su, nan gaba ma kudaden zai tashi daga dubu dari biyu, zuwa dubu dari bakwai koma sama da haka’.
Don haka suke fatan gwamnati zatayi abinda ya kamata, don ganin talaka ya samu ilimi kamar kowanne dan kasa.
You must be logged in to post a comment Login