Kiwon Lafiya
Karin Mutane 20 sun kamu da zazzabin Lassa a Nigeriya- NCDC
Hukumar dakile cututtuka masu yaduwa ta Nijeriya NCDC ta ce, tsakanin 17 da 23 ga watan Afrilun da ya gabata kimanin mutane 20 ne suka kamu da zazzabin Lassa a Nijeriya.
Hakan na cikin rahoton da hukumar ke fitarwa a kowanne mako kan halin da ake ciki game da cutar.
Haka kuma, hukumar ta NCDC ta ce, tun daga farkon shekarar nan da muke ciki zuwa yanzu a kalla mutane 897 ne suka kamu da cutar ta zazzabin Lassa, yayin da mutane 154 suka rasu sanadiyyar cutar a jihohi 26 na Nigeriya.
NCDC ta kuma ce, an gano yadda cutar zazzabin na Lassan ya bazu a jahohin Ondo da Edo da Bauchi da Taraba sai kuma jihar Gombe a cikin mako guda.
You must be logged in to post a comment Login