Connect with us

Labarai

Da dumi-dumi Gwamnan jihar Bauchi ya kamu da COVID-19

Published

on

A dazun nan ne aka tabbatar da cewar, gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad ya kamu da cutar Coronavirus bayan da  sakamakon gwajin da da aka yi masa ya nuna cewa yana dauke da cutar.

Babban mai taimakawa gwamnan na mussaman kan kafafan yada labarai Mukhtar Gidado ya sanar da hakan ga manema labarai cikin wata sanarwar da ya fitar a dazun nan.

Tun da fari gwamnan ya sanar da cewar ya gaisa da Dan tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar Mohammed Atiku wanda shima ya kamu da cutar ta Coronavirus bayan da aka gwada shi a ranar Lahadin da ya gabata.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 335,159 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!