Labarai
Covid-19: KAROTA ta gargadi masu shirin taron daurin aure
Hukumar lura da ababan hawa ta jihar Kano KAROTA ta gargadi wasu iyali dake shirin gudanar da bikin daurin aure a wannan mako.
Cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Sadik Farouk Yola a madadin shugaban hukumar Baffa Babba Danagundi ta ce ta samu wasu iyalai da suka hadar da Alhaji Hassan Badeh, da Alhaji Ibrahim Muhammad da kuma Alhaji Abdullahi Kwamaret Bako, kan su dakatar da shirin su na gudanar da shagalin bikin aure da suke shirin yi.
A cewar KAROTA ta samu labarin cewa za a gayyato baki daga birnin tarayya Abuja da kuma Legas a don hakan take tunasar da su cewa akwai dokar hana cakuduwar jama’a a Kano.
Wakilin mu Nasiru Salisu Zango ya tuntubi Alhaji Ibrahim Badeh daya daga cikin wadanda ke shirin wannan daurin aure, inda ya shaida masa cewa daman basu gayyaci kowa daga wajen Kano ba, daurin auren kadai za a yi a watse, ba tare da cinkoso ba.
Karin labarai:
KAROTA ta kama babbar mota makare da giya
Direbobi sun maka KAROTA da ‘Yan sanda a gaban kotu
You must be logged in to post a comment Login