Kiwon Lafiya
Kasar Amurka ta bukaci Najeriya da ta sauya dabarun yaki da kungiyar boko haram
Kasar Amurka ta bukaci Najeriya da ta sauya dabarun da ta ke amfani da su a yanzu haka wajen yakar yan kungiyar Boko Haram la’akari da yadda mayakan ke kokarin bijirewa dabarun da ake amfani da su.
Guda daga cikin manyan hafsan sojin kasar Amurka da ke halartar taron hafsoshin kasan kasashen Afrika wanda kuma shi ke jagorantar taron da ke ci gaba da gudana a Abuja Laftanal kanal Sean McClure ya ce kamata ya yi a samar da sabbin dabaru matukar ana bukatar gaggauta fattattakar mayakan na Boko Haram.
Amurka dai na neman yin uwa da makarbiya ne waje ganin ta taimakawa kasashen Afrika da gabas ta tsakiya wajen kammala yakar ayyukan ta’addanci.
Kanal McClure ya ce ayyukan ta’addanci a kassahen Afrika da suka kunshi na Boko Haram a Najeriya da Nijar, Kamaru da kuma Chadi da kuma na Al-Qaeda a Mali ka iya zama tarihi matukar aka hada hannu wuri guda.
A baya-bayan nan dai Amurkan na nuna damuwa matuka kan ayyukan ta’addancin da ke faruwa a Nahiyar Afrika, inda ta kaddamar da wani atisayen soji a Jamhuriyar Nijar daga kasashe 26 da suka kunshi 12 na Afrika da kuma 14 daga sauran sassan duniya da nufin yakar ayyukan ta’addanci a yankin Sahel.