Labarai
Kasashen duniya su kawo mana dauki kan sha’anin tsaro – Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci kasashen duniya da su tallafawa Najeriya wajen kawo karshen matsalolin tsaro da ayyukan cin hanci da rashawa har ma da tabarbarewar tattalin arziki.
Wannan dai na cikin wata sanarwa da mai bai wa shugaban kasa shawara kan kafafen yada labarai Femi Adesina ya fitar a Abuja.
Sanarwar na bayyana cewa, shugaba Buhari ya yi wannan kira ne lokacin da yake karbar shaidar kulla yarjejeniyar Diplomasiyya da wasu kasashen duniya.
Cikin jakadun kasashen da suka ziyarci fadar ta shugaban kasa akwai jakadan kasar Gambia Muhammad Njie, da na Korea ta Kudu Kim Young-Chae da kuma na kasar Slovakia Tomas Felix.
Sauran sun hada da: jakadan kasar Bangladesh Masudur Rahman da na Austrelia John Donnelly da na kasar Guinea Bissau Dr Jaao Butiam.
Ta cikin sanarwar Buhari yace akwai bukatar daukar matakai a tsakanin kasashen duniya domin a hada hannu guri guda don kawo karshen matsalolin dake addabar duniya musamman ayyuakan ta’addanci a sassa daban-daban.
You must be logged in to post a comment Login