Labarai
Kashim Shettima ya soki Atiku Abubakar kan caccakar da ya ke yi wa Shugaba Tinubu

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya soki tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, kan caccakar da ya ke yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya na mai tuna ma sa yadda Tinubu ya ba shi damar tsaya wa takarar shugaban ƙasa a shekarar 2007, bayan rikicinsa da jam’iyyar PDP.
Shettima ya bayyana hakan ne yayin wani taron ƙungiyar City Boy Movement da Tinubu a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, inda ya gargaɗi ’yan adawa da su guji abin da ya kira yaɗa ƙarya da hare-haren siyasa kan shugaban ƙasa.
Ya ce, duk da bambancin ra’ayin siyasa, ya kamata ’yan siyasa su riƙa mutunta juna.
A wani ɓangare kuma, Shettima ya ce Tinubu zai sanar da sabbin matakan tallafa wa harkokin noma a makonni masu zuwa, yana mai cewa matakan za su taimaka wajen rage farashin kayan abinci.
Ya kuma kare manufofin sauye-sauyen tattalin arzikin gwamnatin, yana mai cewa duk da wahalhalun da ’yan Najeriya ke fuskanta, akwai alamun ingantuwar tattalin arzikin ƙasar.
You must be logged in to post a comment Login